Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar dandazon Mata sun yi bikin ?ona tsintsiyar Jamiyyar APC A Kaduna sakamakon abin da suka kira matsalar tsaro da wahalar rayuwa da APC ta jefa su a ciki.
Shugaban Jamiyyar PDP na karamar hukumar Birnin Gwari da ke a jihar Alhaji Yarima Mai Taki shi ya jagoranci kona tsintsiyar a lokacin da ya karbi wasu daga cikin matan Jamiyyar APC zuwa Jamiyyar PDP a ranar Lahadi.
Talauci da wahalar rayuwa na cigaba da hauhawa a jihar Kaduna lamarin da masu fashin ba?i ke dangantashi da rashin iya gudanar da mulki na Gwamnan jihar Nasiru El Rufa’i.