Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar dandazon Mata sun yi bikin ƙona tsintsiyar Jam’iyyar APC A Kaduna sakamakon abin da suka kira matsalar tsaro da wahalar rayuwa da APC ta jefa su a ciki.
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birnin Gwari da ke a jihar Alhaji Yarima Mai Taki shi ya jagoranci kona tsintsiyar a lokacin da ya karbi wasu daga cikin matan Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP a ranar Lahadi.
Talauci da wahalar rayuwa na cigaba da hauhawa a jihar Kaduna lamarin da masu fashin baƙi ke dangantashi da rashin iya gudanar da mulki na Gwamnan jihar Nasiru El Rufa’i.