Uwargidan El Rufa’i Ta Ci Gyaran Atiku A Turanci

Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Hajiya Hadiza El Rufa’i ta ci gyaran tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ?an takarar Shugabancin Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a sakon ta’aziyyar da ya aike na rasuwar Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Ahmed Lemu.

Dr Hadiza El-Rufai ta yi wa tsohon Mataimakin shugaban kasar gyara a shafin ta na sada zumunta na Twitter dangane da ?aran?arama da kuma karan tsaye da ya yi a cikin harshen turanci a yayin aikewa da ta’aziyar.

Uwargidar Gwamnan ta nuna akwai katafaren kuskure a wata kalma da Atiku ya yi amfani da ita wadda abin kunya ne ace wannan kuskure ya fito daga bakin Mutum irin Atiku mai han?oron zama Shugaban kasa a babbar kasa irin Najeriya Giwar Afirka.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya na cikin wadanda su ka fara aika ta’aziyyar Marigayi Sheikh Ahmed Lemu wanda ya rasu a makon jiya a gidanshi dake Minna Babban Birnin Jihar Neja.

A sakon ta’aziyyar Atiku Abubakar ya rubuta: “Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Ahmed Lemu, OFR fitaccen Alkali ne, malamin addini, mai tausayin al’umma kuma mai taimakon marasa karfi.”

“Mutuwarsa a lokacin da wadanda ya yi wa bauta har da Najeriya su ke bukatar shawararsa, babbar asara ce. Za a yi kewansa matuka.” Inji Atiku a Twitter.

A jawabin na sa, Atiku Abubakar ya bayyana marigayin da “Humanist”, amma Hadiza Isma-El-Rufai ta ci gyaransa, ta nuna masa cewa ya yi kuskure.

Uwargidar gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Isma-El-Rufai ta nuna Kalmar HUMANIST, abin da ta ke nufi dabam da abin da Atiku Abubakar ya ke tunani. Hadiza El-Rufai ta ce HUMANIST na nufin mutumin da ya yi imani da akidar nan ta humanism.

Dr Hadiza El-Rufai ta ?ara da cewar abin da Kalmar HUMANISM ta ke nufi shi ne mutumin da ya yi imani da karfin ikon Bil Adama a maimakon wani karfin Ubangiji ko halittar boye.

Da alamu abin da Atiku Abubaka yake nufi shi ne Ahmed Lemu ya kasance mai tausayin jama’a da yin abin da al’umma za su amfana.
Amma wasu masana su na ganin cewa Atiku bai yi kuskure ba, domin Kalmar na da wata ma’ana.

Related posts

Leave a Comment