Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Usman Alkali ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin Shugabancin sa ya ?are kamar yadda dokokin kasa suka tanada.
Ministan kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya, Maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a ranar yau Talata.
A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.
Usman Alkali Baba zai karbi ragamar Shugabancin rundunar ‘yan sandan Najeriya ne nan take ba tare da ?ata lokaci ba.