Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya mayar da martani akan wani faifan bidiyo da ke nuna shi ya na zazzagawa matarsa da su ka rabu, Precious Chikwendu, masifa.
Kayode ya garzaya shafinsa na Instagram domin kare kansa a yayin da wasu kafafen yada labarai da ma’abota dandalin sada zumunta ke caccakarsa a kan rashin hakuri da mata.
A cewar tsohon ministan; “Wannan ba wani abu bane face yada farfaganda da son batamin suna. “Babu wani abu a faifan bidiyon sai kokarin da na ke yi na son karbe wayarta ta hannu domin hanata nadar sabanin da muka samu.
“Babu inda aka ganni ina cin zarafinta a faifan bidiyon, hatta fadan da na ke yi saboda na kamata ta ne turmi da tabarya tana cin amanata da wani Ƙato.
“Na kara maimaita cewa ban ci zarafinta ba, ita ce ta ke cin zarafin jama’a, halinta ne cin zarafin jama’a tare da wulalantasu kamar yadda ta ke yi wa ‘yan uwana, ma’aikatana, kananan yara da leburorin da ke aiki gidanmu.
“Za a iya sauraron kalamaina a faifan bidiyon, na fada ma ta cewa kowa zaman lafiya ya ke so amma banda ita. Ban taba cin zarafinta ba duk da na kamata da kwarto,”.