Tura Ta Kai Bango: Gwamnatin Tarayya Zata Buɗe Makarantu

Gwamnatin tarayyar ta fito da sharuda na sake bude makarantu domin ‘daliban da ake shirin za su koma aji kwanan nan. Sai dai gwamnatin kasar ba ta bayyana lokutan da ‘yan makarantan za su koma bakin karatu ba.

Tsare-tsaren da aka fito da su, su na kunshe da sharuda da matakai da ake bukata kafin a iya daukar darasi ko shiga aji a lokacin annobar COVID-19. Kamar yadda ma’aikatar ilmi ta kasa ta bayyana a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, za a rika bada tazara a wurin karatu idan an bude makarantun boko.

Jawabin ya nuna cewa za a rika samun ratar akalla mita biyu tsakanin masu daukar karatu da ma’aikatan makaranta a cikin aji da sauran dakunan karatu. Mai girma ministan ilmi, Mallam Adamu Adamu da karamin ministan ilmi na tarayya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba su ka sa hannu a wannan takarda.

Ma’aikatar ilmi ta dauki wannan mataki ne tare da ma’aikatar muhalli, da ta lafiya, da kuma sauran masana kiwon lafiya a Najeriya. A takardar, an bayyana cewa: “Sai dai akwai lokutan da ba zai yiwu a dabbaka dokar tazarar mita biyu ba, don haka za a iya kawo wasu dabaru na daban.”

Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi kokarin kare lafiyar ‘yan makaranta ta hanyar raba dalibai zuwa kananan sahu-sahu inda za a tabbatar an bi matakan kare kai. “Da fitowar wannan takarda, gwamnati za ta gudanar da bincike domin fahimtar abin da ake bukata wajen fadada wuraren daukar karatu da kayan aiki irinsu tebura, kujeru, ruwa, man wanke hannu, na’urorin zamani da sauransu.”

Da wadannan kayan aiki da wasu tsare-tsaren ne hukuma za ta amince a sake bude makarantu domin cigaba da karatu. Gwamnati ta ce lokaci ya yi da za a tsara yadda za a bude makarantu. Da ya ke jawabi, Adamu Adamu ya ce hakan ya zama dole tun da za a dade ana fama da COVID-19.

Labarai Makamanta

Leave a Reply