Tsohon Ka Nake Jira- Amsar Gabon Ga Wanda Ya Tambayeta Yaushe Za Ta Yi Aure

Hadiza Gabon, tauraruwar fina-finan Hausa ce dai wacce kusan kowa ya santa, ta baiwa masoyanta damar yi mata tambayoyi inda ita kuma ta basu amsa.

Sai dai mun samu damar kawo muku kaɗan daga cikin tambayoyin masu ɗaukar hankali da aka mata kuma ta bada amsarsu.

– Wane gari kaka fi so a Najeriya? Ta bada Amsar cewa “Na fi son Kaduna”.

– Wani ya tambayeta idan ya nemeta da aure zata yadda? Tace masa a’a.

– Kazalika wani ya tambayi Gabon ‘yau she za’a yi wuf da ke?’ Sai ta bashi amsar cewa ”Tsoho ya shirya?”

– Wani ya tambayeta zata yadda ta yi soyayya dashi? Sai tace a’a?

– Wani ya tambayeta yaushe zaki yi aure? Sai tace masa “Yaushe zaka mutu”?

– Wani ya tambayeta, bayan fim, wace harka take yi tana samun kudi? Sai tace sana’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply