Shahararren shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji ya zargi karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu wajen tallafawa ta’addanci a Najeriya.
Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, sanannen dan ta’adda ne kuma shugaban ‘yan fashi da makami wanda ya yi ta kai hare-hare a jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Zamfara, Sokoto da Niger.
Ana zargin shugaban ‘yan ta’addan mai shekaru 28 da haihuwa ya jagoranci wasu ‘yan bindiga daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Janairun 2022, inda ‘yan bindiga suka kashe sama da mutane 200 da suka hada da mata da kananan yara a jihar Zamfara.
Turji, a wani sabon faifan bidiyo da SaharaReporters ta samu ya yi zargin cewa batun rashin tsaro da ya addabi kasar nan na da cikakken goyon bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma karamin ministan tsaro na yanzu.
Ya ce yana da shaidun da ke tabbatar da wannan ikirari, inda ya ce gwamnatin da ta shude, a karkashin Matawalle ta san kowa a yankin.
Da yake magana da harshen Hausa, ya ce, “Sunana Muhammed Bello Turji, kuma na fitar da wannan bidiyon ne domin in isa ga daukacin ‘yan Nijeriya, tun daga shugabanni har zuwa talakawa. Wannan shine sakon da nake so in isar wa kowa
“Batun rashin tsaro da ya addabi kasarmu yana da cikakken goyon bayan gwamnatin da ta shude a jihar Zamfara. Ina da shaidar da za ta goyi bayan wannan ikirari. Gwamnatin da ta shude, karkashin Mai Girma Bello Mattawallen Maradun ( Karamin Ministan Tsaro), sananne ne ga kowa da kowa a yankin.
“Wannan gwamnati ta kasance mai hadin kai wajen tallafawa ta’addanci. Akwai mutane daga Shinkafi, Zurmi, da Issah da ba za su iya musun wannan bidiyo ba.
“Yawancin ‘yan Najeriya, misali wadanda ke Bauchi ko Kaduna, watakila ba su san matsalolin da ke faruwa a Zamfara ba. Duk da haka, ina so in tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa idan ba su sani ba, zan ba da sunaye, cikakkun bayanai, da kuma shaidu. Ina kira gare su da su binciki abubuwan da wadannan mutane suka yi a baya da kuma tattaunawar da suka yi da su. A matsayina na dan wannan shiyyar, (Arewa maso Yamma) na rantse a gaban Allah cewa na fadi gaskiya.
“Gwamnatin Zamfara da ta shude, karkashin Mattawalle, ta taimaka wajen tattaunawa amma kuma ta yi zagon kasa. An yi tataunawa da yawa, amma tattaunawar ba ta yi nasara ba domin kowa a Shinkafi da Isah ya san gaskiya. Misali Marigayi Dillu na kore shi ne saboda ya ki yarda a yi zaman lafiya a Shinkafi. Sun mallaki bindigogi sama da 200, kuma Mattawalle ya gayyace su gidan gwamnati. Idan karya nake, har yanzu akwai mutane a gidan gwamnati da za su iya bayyana wannan.
“Lokacin da muka kashe Dillu, ya kamata Kabiru Maniya ya bayyana inda gwamnatin tarayya ko ta Zamfara da Sokoto suka tattauna da shi domin ya ajiye makamansa. Shi ma Bashir Maniya ya kamata ya gaya mana inda yake boye makamansa. Kowa ya san suna da bindigu sama da 300, wanda na karbo 30 daga cikinsu. Su fito su fadi gaskiyar abin da ke faruwa.
“Kamar yadda muke magana, suna cikin garin Sakkwato. Jama’a irin su Malam Murtala Asada (Malamin Islama) na ta fadin cewa akwai wasu ’yan Turji (’yan bindiga) da ke yawo cikin walwala a cikin birnin Sakkwato, inda suke nuni da Maniya da tawagarsa wadanda ake zaton sun boye bindigogi sama da 300 a wani wuri.
“Akwai shugabannin ‘yan fashi da ‘ya’yansu dake boye a unguwanni daban-daban dauke da bindigogi daga 150 zuwa 300, amma a yanzu sun yi ikirarin cewa suna aiki da sojojin gwamnati a matsayin tuba. Kuma a duk lokacin da ‘yan fashin suka so kai hari a ko’ina, za su shawarci jami’an tsaro da su bar yankunan Sakkwato domin a samu damar kai hare-hare. Idan karya nake yi, ya kamata mutanen Mai Lalle su fito su yi musun cewa ba a kullum ake kai musu hari ba.
“’Yan bindigar da suka kai musu hari sun fito ne daga yankin Shehu da ke dajin Gonbro, a Sakkwato. Dan Maigari dan uwan Bashari yana da bindigu 150 kuma ya hada kai hare-hare da dama a Maradun. Ali, yaro ga Kabiru Mani, yana kai hari Tangaza, kuma wadannan mutane ne da ke zaune cikin walwala a babban birnin jihar Sokoto. Kabiru, Buhari, da sauran su suna rayuwa mai dadi a Sakkwato.
“A cikin makonni uku da suka gabata, an ce dan’uwan Buhari ya kama makami a cikin Sakkwato. Idan karya nake yi, su fito su karyata. Amma zan iya bayar da hujjar Buhari ya harbi GPMG. Su bayyana mana wadanda suka ba wa wadannan yaran makaman da suke amfani da su. Ya kamata gwamnati ta bayyana wa ’yan Najeriya wannan batu, ta daina zargin Bello Turji da kashe mutane da sace mutane. Wadanda ake garkuwa da su a kewayen Sakkwato, Achida, da Goronyo—wa ke sace su? Turji, a halin yanzu yana zaune lafiya a Shinkafi, ba shi da alhaki.
“Bari gwamnati ta fito ta dauki alhakin wasu ta’addancin da ake yi, ta daina zargin wasu da karya.”
A shekarar 2022, SaharaReporters ta ruwaito musamman yadda Matawalle a matsayin gwamnan Zamfara ya bayar da tallafin sabbin motoci kirar Hilux guda 15 ga shugabannin kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban na jihar.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun hada da Na Shama, Sani Shaidan, Mohammadu Bello Halilu da Bage Waye.
Sauran ‘yan fashin da suka samu motocin sun hada da Kachalla, Ado, Busniya, Dunbulu da Gajere.
SaharaReporters ta samu labarin cewa tsohon gwamnan ya kuma amince da miliyoyin nairori da za a baiwa ‘yan fashin da suka tuba a matsayin diyya.