Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufa’i Ya Yi Amai Ya Lashe

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya yi ƙarin haske kan kalaman da ya yi ana dab da rantsar da sabuwar gwamnati

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa wasu ne kawai marasa son gaskiya suka sauya haƙiƙanin ma’anar kalaman da ya yi a lokacin Ya nesanta kansa ce da faɗin Shugaba Tinubu da addini ya yi amfani wajen lashe mulkin shugabancin ƙasar nan

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya nesanta kansa da cewa ya yi kalaman da ke cewa Shugaba Tinubu ya yi amfani da addini wajen cin zaɓen ƙasar nan.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ƙarya ce kawai tsagwaronta wacce aka ƙirƙiro ake jifansa da ita, rahoton The Cable ya tabbatar.

Da yake magana a wajen ƙaddamar da wani littafi a wajen bikin ritayar Farfesa Ishaq Akintola na jami’ar jihar Legas, tsohon gwamnan ya ce ya ƙi yin martani kan sauya masa kalamai da aka yi ne saboda waɗanda suka yi hakan basu son gaskiya.

El-Rufai ya bayyana cewa kalaman nasa da ya yi ana dab da rantsar da sabuwar gwamnati kan siyasa da mulki a jihar Kaduna da batun tikitin Asiwaju-Shettima kamata ya yi ace an fahimcesu da idon basira.

El-Rufai ya nuna godiyarsa kan waɗanda suka goyi bayansa a lokacin Tsohon gwamnan ya nuna godiyarsa ga ƙungiyar MURIC da sauran waɗanda suka riƙa kare shi ta hanyar bayyana haƙiƙanin saƙon da yake nufi a cikin kalaman da ya yi a wancan lokacin, cewar rahoton

A kalamansa: “Na yanke shawarar ba zan taɓa martani kan murɗe gaskiya da ƙarairayi na batun musuluntar da ƙasa da ire-irensu saboda waɗanda ke yin wannan ƙagen za su yi ta yi ne saboda basu ganin ƙimar gaskiya da daidaituwa.” “

“Sun riga da sun gama yanke hukunci kan saƙon da wanda ya isar da shi ko da kuwa na yi magana ko ban yi ba.”

Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai “Ga waɗanda su ke son sanin gaskiya, saƙo na a Kaduna shi ne shugabanci yana ginuwa ne kan turbar gaskiya da adalci (a musulunci ko kiristanci), sannan dole shugaba ya yi adalci ga kowa, musulmi da kirista ko wanda ba haka ba.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply