Rahotanni daga jihar Anambra na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ?auke da manyan Bindigogi sun budewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, wuta.
‘Yan Bindigar sun yi nasarar kashe jami’an yan sanda uku dake gadinsa, sannan suka raunata wasu jama’a da dama.
Wannan hari ya faru ne a garin Isuofa, a karamar hukumar Aguata a jihar Anambra yayinda yaje ganawa da wasu matasa a yankin a cigaba da tallata kanshi da yake yi na takarar gwamnan Jihar.
Shaidun gani da ido sun bayyanawa ‘yan Jarida cewa Soludo na cikin koshin lafiya, babu abinda ya samesa a yayin kai harin.
Wasu rahotanni sun bayyanawa cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da kwamishanan kayakkayin jihar, Emeka Ezenwanne da wasu mutane.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace rundunar tana nan tana gudanar da bincike.