An kwantar da shahararren dan kwallon Brazil Pele a asibiti amma ƴarsa ta ce baya cikin mummunan yanayi.
Tashar ESPN Brasil ta bada rahoton cewa an garzaya da Pele zuwa asibitin Albert Einstein da ke birnin Sao Paulo saboda yana fama da kumburi a jikinsa.
Amma diyar Pele din Kely Nascimento ta wallafa a shafinta na Instagram cewar jikin bai yi tsanani ba.
A watan Satumbar 2021 ne aka yi wa Pele tiyata kuma tun daga lokacin ake yawan kwantar da shi a asibiti.
ESPN Brasil ta bada rahoton cewa dan shekaru 82 din yana fama da matsalar ciwon zuciya.
Pele shi ne ya fi kowanne dan Brazil cin kwallo inda ya zura kwallo 77 a cikin wasa 92 kuma yana cikin ‘yan wasa hudu da suka ci kwallo a gasar cin kofin duniya hudu a jere.