Tsigaggen Wazirin Bauchi Ya Sha Alwashin Daukar Fansa Kan Gwamna

Tsohon Wazirin Bauchi da gwamnatin jihar ta tube masa rawani, Alh. Muhammadu Bello Kirfi ya lashi takobin kawar da gwamnan jihar, Bala Mohammed daga kujerarsa ta gwamna kamar dai yadda ya kawo shi kan madafun iko a cewarsa.

A karon farko kenan da tsohon Wazirin na Bauchi ke mayar da martani irin wannan tun bayan da gwamnatin jihar ta tube masa rawani bayan ta zarge shi da nuna rashin da’a ga gwamna.

Kirfi ya shaida wa manema labarai a gidansa cewa, yana daya daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi makarmiya wajen kawo gwamnan kan kujerarsa, yana mai bayyana takaicinsa kan matakin da gwamnan ya dauka a kansa.

Wannan ne cin mutunci mafi girma da zai yi min, amma babu damuwa saboda ba na samun ribar komai daga sarautar ta Waziri da nake rike da ita a fada” inji Kirfi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply