Ministan tsaron Najeriya Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya bayyana cewar tsaro ya dawo kuma ya ?ara inganta a Najeriya ?ar?ashin jagorancin mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, duk da wasu ‘yan matsaloli da ake fuskanta a wasu wuraren.
Ministan ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Harkokin Tsaro na Sojoji, Sanata Aliyu Wamakko ya kai ziyarar duba-gari a Ofishin shi dake birnin tarayya Abuja.
Manjo Janar Magashi mai ritaya, ya ?ara da cewar duk da yake Najeriya na ta fama da kalubalen matsalolin tsaro a cikin gida, ya yi tsinkayen cewa an samu dawo da zaman lafiya a wasu sassan kasar nan, inda masu garkuwa da mutane su ka rika kai hare-hare a baya.
“Najeriya na fama da matsalolin tsaro daban-daban, inda Boko Haram da ’yan bindiga ke ci gaba da amfani da muggan makamai a jihohin Neja, Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara.”
“Sojojin Najeriya na ci gaba da dakile wannan barazana ta gabagadi a sassan kasar nan, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
“Wadannan kalubale sun haifar da asarar rayukan zaratan sojojin Najeriya masu tsantsar kishin kasa da su ka sadaukar da rayuwar su ga kasar nan.
“Amma kuma duk da wannan kalubale, sojojin Najeriya sun samu nasarar wanzar da zaman lafiya a wasu sassan kasar nan.” Inji Magashi.