Tsaro Ya Samu A Mulkin Buhari Fiye Da Gwamnatocin Baya – Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa jami’an tsaro na aiki tukuru don kare rayukan ‘yan Nijeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, Ministan ya kara da cewa, yanayin tsaron Nijeriya a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya fi na gwamnatocin da suka gabata inganci.

Lai Mohammed ya kuma ya bayyana wasu nasarorin da jami’an tsaro suka samu yayin gudanar da ayyukansu.

Ya ce: “Zan iya fada ba tare da jinkiri ba cewa, duk da cewa Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro, lamarin ya fi abin da muka hadu da shi a 2015 kyau.

“Zan iya fada muku a yau cewa sojoji,‘ yan sanda da sauran jami’an tsaro da na leken asiri suna kara kaimi don bunkasa tsaron rayuka da dukiyoyi a duk fadin kasar, kuma sakamakon ya fara nunawa.

“Saboda haka, za mu nuna, a wannan taron manema labarai, nasarorin da aka samu kwanan nan da Sojoji da sauran jami’an tsaro da hukumomin leken asiri suka yi a yaki da‘ yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran masu laifi.

“Tun daga farkon wannan shekarar, wanda ya cika kimanin makonni uku da kafuwa, Sojojin Najeriya sun kashe masu aikata laifuka 158 a duk fadin kasar. Wannan kari ne ga dinbin wasu ‘yan ta’adda da’ yan fashi da makami da aka kashe yayin hare-hare ta sama.

“An kama wasu masu laifi 52, tare da dimbin makamai, alburusai da kayan aiki.

“Sojojin sun kuma ceto jimillar mutane 17 da aka yi garkuwa da su a duk fadin kasar.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply