Tsaro: Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Mallaki Bindigogi Domin Kare Kai- Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya ta bai wa `yan kasar da suka mallaki hankali lasisin mallakar bindiga samfurin AK47 domin su kare kansu daga hare-haren da miyagu ke kaiwa.

Gwamnan ya ce ba da lasisin ne kawai mafita, saboda manyan makaman da ke hannun miyagu sun fi karfin bindigar da doka ta ba da izinin mallaka.

Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya yi wannan bayanin ne a cikin wata kasidar da ya gabatar a wani taron gwamnonin Najeriya da aka yi ta intanet.

Ya kara da cewa jamian tsaron Najeriya na bakin kokarinsu, amma aiki na nema ya gagari kundila idan aka yi lakari da hare-haren da yan boko haram dayan bindiga masu satar mutane ke kai wa a sassan kasar daban-daban.

Don haka ne yake ganin cewa ya kamata a bar `yan kasa su ma su mallake su:

“Ya kamata a baiwa jama`a damar mallakar manyan makamai irin bindiga samfurin AK47, kamar yadda wadannan miyagun suke da ita. Idan gwamnati ta ba da wannan lasisin, mutane za su samu damar ajiye bindigogin a gida ta yadda za su iya tunkarar wadannan miyagu idan suka kai musu hari”, in ji Gwamna Ortom.

Sai dai masana harkokin tsaro na baya-baya da wannan batun. Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce ba alheri ba ne.

A Najeriya dai za a iya cewa ana tsaka mai wuya, ko gaba kura baya sayaki, wato miyagu za su ci gaba da cutar da alumma idanyan kasa suka ci gaba da zama babu abin kare kai, haka kuma tsaron ka iya kara tabarbarewa idan aka yi rashin sa`a makaman suka shiga hannun da bai dace ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply