Tsaro Ya Inganta A Najeriya Karkashin Shugabanci Na – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu nasara ainun wajen shawo kan matsaloin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin ritayar tutoci 53 da aka gudanar na rundunar sojojin kasar.

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari ya bayyana irin dimbin kalubalen tsaro da ya taras lokacin da ya amshi mulkin Najeriya shekaru takwas da suka gabata. da suka hada da, murkushe mayakan Boko Haram, ceto wadanda mayakan su ka yi garkuwa da su da dama, da kuma shawo kai da sake tsugunar da daruruwan mayaka da su ka ajiya makamai su ka mika wuya.

Da yake tsokaci kan irin yadda aka tunkari matsalar tsaron tun farko, Shugaba Buhari yace, jim kadan bayan hawansa mulki, sun sami nasarar shawo kan matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa, yan aware, masu satar mai da sauran masu aikata manyan laifuka.

Janar Buhari yace cikin shekaru takwas da yayi yana mulki, ya bada umarnin daukar zaratan sojoji sama da dubu sittin, banda dubban hafsoshin da kowacce shekara ake yayewa daga makarantar horas da hafsoshi ta kaduna.

Dangane kuma da batun kayan aiki, Shugaba Buhari yace bayan irin hobbasan da yayi na samarwa sojojin daruruwan motocin sulke da harsasai basa iya ratsa su, da sauran kayayyakin aikin soji, an kuma sayi jiragen sama na aikin soji na zamani, tare da horas da jami’an sojin a fannin amfani da kuma kula da su.

Ya kara da cewa, an samarwa sojojin manyan bindigogin Artillary,
bindigogi masu sarrafa kansu, da dimbin harsasai daban daban da suka yi matukar tisiri a sauya rawar da sojojin Najeriya ke takawa wajen fuskantar kalubalen tsaro.

Related posts

Leave a Comment