Tsaro: Sojojin Najeriya Ihu Bayan Hari Suke Yi – El Rufa’i

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce shi da sauran gwamnoni “hannunsu a ?aure yake” game da yadda ake gudanar da harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihohinsu.

Gwamnan na magana ne ta cikin shirin Politics Today a kafar Channels TV a yammacin yau, yana mai cewa ba su da wani iko mai yawa.

“Hannuna a ?aure yake a jihata. Gwamnoni da yawa hannunsu a ?aure yake. Ana kiranmu shugabannin tsaro (chief security officers) a suna kawai amma ba mu da wani iko kan manyan abubuwa…kusan babu yadda muka iya,” in ji shi.

El-rufai wanda yanzu haka yake birnin Dubai ya ci gaba da cewa: “Mu [gwamnoni] mun fa?a wa shugaban ?asa da mataimakinsa…ana ta gudanar da ayyukan sojoji amma sai an kai hari sannan suke aiki.”

Related posts

Leave a Comment