Sojojin sama na Operation Thunder Strike sun kai hari a sansanin ƴan bindiga a dajin Kuduru da Kuyambana. Sojojin ta hanyar amfani da jiragen yaƙi sunyi nasarar halaka ƴan bindiga da dama tare da lalata gine-ginensu Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Thunder Strike sun kashe ƴan bindiga masu yawa a harin da ta kai sansaninsu da ke dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.
” Kakakin rundunar ta musamman, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin rundunar na Twitter a ranar Juma’a a Abuja. Ya ce dakarun sojojin sun samu wannan nasarorin ne sakamakon hare-haren da suka kai a ranakun Laraba da Alhamis.
Enenche ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna yan ta’addan na amfani da wuraren don shirya kai hari kafin aka far musu. Ya ce an kai harin a maɓuyar ƴan ta’addan a dajin Kuduru ne da na’urar leƙen asiri daya nuna akwai ƴan bindiga da dama a cikin gine-ginen da ke dajin.
“Jiragen yaƙin sun yi ta ruwan bama-bamai ɗaya bayan ɗaya a inda gine-ginen suke inda suka kashe da dama tare da lalata sansanin.
“A dajin Kuyambana ne muka hango wasu ƴan bindiga tare da shanu da suka sace kusa da wasu bukoki, jiragen NAF da jirage masu saukan ungulu sun musu ruwan wuta inda suka yi nasarar kashe mutane da dama cikin su,” in ji shi.