An yi tir gami da Allah wadai da yadda harkar tsaro ke ƙara shiga cikin ruɗani a ƙasar nan musamman a yankin Arewacin ƙasar, amma abin takaici shugabannin sun yi gum babu shugabanci a yankin.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kwalejin tunawa da Sardauna wato SMC Imam Sa’id Abubakar ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da huɗubar sallar juma’a a masallacin a yau.
Limamin ya ƙara da cewar da akwai alamu da suka nuna cewar da akwai wani shiri da ake da shi na shafe jama’ar Arewa a doron ƙasa, dalili kuwa shine dukkanin sauran yankunan ƙasar na zaune lafiya amma da zarar an shigo yankin arewacin Najeriya sai a ga al’amurra sun canza ana kisan jama’a kisa irin na kiyashi.
Limam Sa’id Abubakar ya ce babu inda aka farlanta yin shugabanci dole, idan mutum ya san ba zai iya ba to ya gaggauta sauka wadanda zasu iya kare rayuka da dukiyoyin jama’a su amsa.
“An ƙiyasta cewa sama da mutane 1500 ne aka yi wa kisan gilla cikin watanni shida a jihohin Katsina da Zamfara, ko Kaji ake kisa haka ai abin a duba ne ballantana mutane Musulmi masu bautar Allah, babu shakka shugabanni a Najeriya sun gaza”.
Imam Abubakar ya yi addu’ar Allah ya tona Asirin dukkanin wani ɗan siyasa ko ma’aikacin tsaro ko ma waye da ke da hannu a kashe kashen da ke faruwa a yankin Arewacin Najeriya.