Tsaro: Shugabannin Najeriya Sun Gaza – Limamin SMC Kaduna

An yi tir gami da Allah wadai da yadda harkar tsaro ke ?ara shiga cikin ru?ani a ?asar nan musamman a yankin Arewacin ?asar, amma abin takaici shugabannin sun yi gum babu shugabanci a yankin.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kwalejin tunawa da Sardauna wato SMC Imam Sa’id Abubakar ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da hu?ubar sallar juma’a a masallacin a yau.

Limamin ya ?ara da cewar da akwai alamu da suka nuna cewar da akwai wani shiri da ake da shi na shafe jama’ar Arewa a doron ?asa, dalili kuwa shine dukkanin sauran yankunan ?asar na zaune lafiya amma da zarar an shigo yankin arewacin Najeriya sai a ga al’amurra sun canza ana kisan jama’a kisa irin na kiyashi.

Limam Sa’id Abubakar ya ce babu inda aka farlanta yin shugabanci dole, idan mutum ya san ba zai iya ba to ya gaggauta sauka wadanda zasu iya kare rayuka da dukiyoyin jama’a su amsa.

“An ?iyasta cewa sama da mutane 1500 ne aka yi wa kisan gilla cikin watanni shida a jihohin Katsina da Zamfara, ko Kaji ake kisa haka ai abin a duba ne ballantana mutane Musulmi masu bautar Allah, babu shakka shugabanni a Najeriya sun gaza”.

Imam Abubakar ya yi addu’ar Allah ya tona Asirin dukkanin wani ?an siyasa ko ma’aikacin tsaro ko ma waye da ke da hannu a kashe kashen da ke faruwa a yankin Arewacin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment