Shugaban Kwamitin Rundunar Sojoji ta Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya ce rashin isasun kudi da sojoji ke fama da shi ne yasa bai nemi a sauke shugabannin hafsoshin tsaron daga mukamansu ba.
Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawar ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa bai bayar da shawarar a sauke shugabannin hukumomin tsaron ba a kudirinsa na farko domin ya san rundunar tana fama da karancin kudi.
Dan majalisar ya yi wannan bayanin ne bayan Majalisar Dattawar ta cimma matsayar cewa Shugabanin hukumomin tsaron su yi murabus saboda kisar sojoji tare da murabus din fiye da 200.
Duk da cewa ainihin kudirin da Ndume ya gabatar wa majalisa ba ta nemi a sauke shugabannin hukumomin tsaron ba, Sanata Francin Fadahunsi (PDP, Osun) ya yi wa kudirin kwaskwarima ya kara hakan.
Sai dai Majalisar ta ce wannan matakin da ta dauka ne kira ga shugabanin hukumomin tsaron su yi murabus shawara ce kawai ga shugaban kasar ba wai doka ba ce da kotu za ta iya zartarwa.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan zaman majalisar a ranar Talara, Kakakin Majalisae, Sanata Ajibola Basiru ya ce bai kamata ayi watsi da shawarar da suka bayar din ba.
“Bai kamata ayi watsi da shawarar da zababun yan majalisar Najeriya suka bawa Shugaban kasa ba duk da cewa ba doka bace,” in ji shi.
Ya kamata a dauki shawarar da matukar muhimmanci kuma ta zama abin lura musamman a kan batun yaki da taadanci a cewar dan majalisar.
A wani labarin daban, kun ji ‘yan bindiga sun kashe dagajin kauyen Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna da wasu mutane tara.
Wannan na zuwa na kimanin awa 24 bayan kashe wasu matasa 21 yayin bikin daurin aure a kauyen Kukum Daji da ke karamar hukumar Kaura.
The Nation ta ruwaito cewa har da wani yaro mai shekara shida cikin wadanda aka kashe a harin na baya bayan nan tare da jikkata wasu mutane da dama.
Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce yan bindiga kimanin su 20 ne suka kai farmaki kauyen misalin karfe 7 na yamma a ranar Litinin suka fara harbe harbe.