‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun jaddada bukatar gudanar da bincike a kan wani wasu sojoji 365 da suka ajiye aikinsu lokaci ɗaya.
Hukumomin sojin ƙasar dai sun ce akan ba wa sojoji masu buƙata damar yin irin wannan murabus din daga lokaci zuwa lokaci mma `yan majalisar sun musanta, suna cewa ba a taɓa samun sojojin da yawansu ya kai bataliya sun yi ritaya karo ɗaya ba.
Hon Muhammad Tahir Monguno babban mai tsawatarwa a majalisar kuma shi ne ya gabatar da kudurin da majalisar ta amince don gudanar da bincike, ya shaida wa BBC cewa matsaloli ne kawai suke tilasta wa sojojin yin murabus.
A ƙarshen da ya gabata ne rahotanni suka ambato cewa sojoji 350 za su ajiye aikinsu na soja saboda sun gaji da aikin bisa wasu dalilai na rashin gamsuwa da shugabancin rundunar.
Haka kuma ƙarancin albashi da rashin kayan aiki da ma rashin karfafa masu gwiwa na daga cikin batutuwan da ƙananan sojojin da ke yaƙi da Boko Haram suka koka a kai.