Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tsaro: Ku Kara Zage Damtse Kokarin Ku Ya Gaza – Buhari Ga Shugabannin Tsaro

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bukaci shuwagabannin tsaro da su tabbatar suna bin umarnin da yake basu sau da kafa inda ya kara da cewa kokarinsu bai gamsar ba.

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a NTA inda yace yana zama da shuwagabannin tsaron daga lokaci zuwa lokaci kuma yana gaya musu cewa su rika bin abinda yace fada.

Yace babban aikinsu shine samar da tsaron Rayuwa da Dukiya ga kowa amma ba su kai ga samun nasarar yin hakan ba. Yace amma suna ci gaba da kokari.

Shugaban kasa dai na cigaba da fuskantar matsin lamba akan lallai sai ya kori shugabannin tsaron ƙasar waɗanda akasarin ‘yan Najeriya ke kallon sun gaza wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, duba da yadda ‘yan ta’adda ke cigaba da cin karen su babu babbaka a kasar musanman sashin Arewacin kasar.

Kiran baya bayan nan dai shine wanda mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya yi, inda ya yi kira ga Buhari da ya yi gaggawar sallamar Shugabannin Tsaron.

Harkar tsaro dai a Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar na cigaba da fuskantar koma baya a kusan kullum, Boko Haram na kisan jama’a a yankin arewa maso gabas yayin da ‘yan Bindiga ke hallaka mutane a sashin Arewa maso yammacin kasar.

Exit mobile version