Tsaro: Ka Sanya Tsofaffin Shugabanni Domin Shawo Kan Matsalar – Sani Ga Buhari

Tsohon Sanata daga Jihar Kaduna Kwamred Shehu Sani, ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa kwamitin da zai warware matsalolin kabilanci da rigingimu saboda banbancin addini ko ƙabila a yankin Arewa.

Da ya ke bayar da wannan shawara a ranar Litinin, Shehu Sani ya ce kwamitin ya kamata ya kunsh tsofaffin shugabannin ƙasai Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar, sannan a sanya Farfesa Jubril Aminu, da Audu Ogbeh, a matsayin jagorori.

Tsohon Sanatan ya bukaci shugaba Buhari ya mayar da hankali a kan warware matsalolin arewacin Najeriya, sannan ya kara da cewa; “yankin kudu ba ya fuskantar kalubalen tsaro saboda matsalolin banbancin addini ko ƙabila.

“Ya kamata shugaba Buhari ya wakilta Janar Gowon, Abdulsalami Abubakar, Audu Ogbeh, da Farfesa Jubril Aminu domin su bullo da sabbin hanyoyin kawo karshen rigingimu ma su nasaba da kabilanci da banbacin addini da kuma rikicin manoma da makiya domin dawo da zaman lafiya a yankin arewa,”.

Sanna ya kara da cewa; “yankin kudancin Najeriya ba ya fuskantar kalubalen tsaro saboda matsalolin banbancin addini ko ƙabila.”

A ‘yan shekaru baya bayan nan, jihohin arewa da dama sun tsinci kansu a cikin matsalolin rashin tsaro da suka hada da rikicin manoma da makiyaya, barnar dukiya da rayuka da ‘yan bindiga ke yi, garkuwa da mutane da sauransu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply