Tsaro: Jihar Kaduna Na Buƙatar Addu’a -Shehu Sani

Tsohon sanata mai wakiltan mazabar kaduna ta tsakiya kuma ‘dan rajin kare haqqin bil’adama, kwamrade Shehu Sani ya bayyana cewa ” yawaitar ayyukan ta’addanci da kullum yake karuwa a jihar ba bukatar komawa ga Allah domin niman mafita.

Sanatan ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan samun labarin sace daliban makaranta da akayi a kauyen Danba-Kasaya dake karamar hukumar chikun.

‘Yan bindigar sun sace daliban ne a makarantar Prince academy dake kauyen tare da kashe mutum daya, inda wasu ruhotanni ke cewa sunyi garkuwa da wasu mutanen kauyen a yayin harin.

TsaroShehu Sani yace jihar Kaduna dama sauran jihohin dake fama da matsalar ta’addanci babu abinda suke bukata a halin yanzu da ya wuce addu’a da kuma kara bullo da sabbin dabaru a yakin da akeyi da ta’addanci domin kawo karshen matsalar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply