Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bukaci hukumar yan sanda da ta tura jami’an rundunar SARS da aka rushe zuwa jihar domin bayar da gudunmawa a yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Babagana ya yi wannan rokon a ranar talata, a yayin wata sanarwa da ofishin Gwamnan ya bayar a babban birnin Jihar Maiduguri, kuma aka rarraba shi ga manema labarai.
An dai soke sashin rundunar ta ‘yan sanda sannan aka rarraba jami’anta zuwa wasu bangarorin biyo bayan zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar a kasar.
Kasa da kwanaki biyu bayan soke rundunar ‘yan sandan, an sake gudanar da gagarumar zanga-zanga kan ayyukanta a ranar Talata a fadin kasar.
Zulum ya yi kiran ne a lokacin da wata tawaga karkashin jagorancin ministan cikin gida, Rauf Argebesola suka gana da shi a gidan gwamnati dake Maiduguri.
Gwamnan ya ce jami’an rundunar da aka soke sun taka muhimmiyar rawar gani a ayyukan yaki da ta’addanci da karfinsu musamman a yaki da Boko Haram.
“Ba ma goyon bayan cin zarafi daga kowane jami’in tsaro, amma maganar gaskiya, a nan jihar Borno bai kamata a wofantar da kokarin jami’an SARS ba a yaki da suke da ta’addanci.
“Suna kokari matuka wajen magance matsalar tsaro a jihar Borno. Sun taimakawa kokarin rundunar sojin Najeriya sosai”.
Wasu kungiyoyin jama’a da na ‘yan kasuwa a jihar Borno sun fito unguwa don yi zanga-zangar rashin jin dadi ruguza rundunar yan sandan SARS da gwamnatin Tarayya ta yi.
Masu zanga-zangar na so rundunar SARS ta ci gaba da ayyukanta a jihar Borno. Shugaban gamayyar kungiyar a Borno, Ahmed Shehu, ya ce koda dai basa farin ciki da Abunda ke gudana a wasu sassan kasar, “jami’an SARS sun taimaka sosai wajen yaki da ta’addanci.