Gwamnonin Zamfara da Neja, a ranar Alhamis, sun ziyarci mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Gwamna Lawal ya kai wannan ziyarar ne tare da gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago a ƙoƙarinsu na samar da ingantacciyar zaman lafiya a jihohinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya jaddada cewa gwamnonin sun yi tattaunawar ne a keɓe a ofishin na Mallam Nuhu Ribadu dake Abuja.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal na cike da damuwa da matsalar tsaron da ke addabar Zamfara.
Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal da Gwamna Mohammed Umar Bago sun ziyarci Mallam Nuhu Ribadu ne a yunkurinsu na kyautata alaƙa tsakanin jihohin da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro.
“Dawo da zaman lafiya a Jihar Zamfara shi ne abu mafi muhimmanci ga Gwamna Dauda Lawal tun bayan da ya zamo gwamnan Jihar.
“A wurin tattaunawar, gwamnonin sun samu fahimtar juna tare da Mallam Nuhu Ribadu kan muhimman batutuwa na tsaro.”