Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin Antoni Janar na Tarayya ta tuhumi shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore Bello Bodejo da laifin kafa kungiyar tsaro ta sa-kai ba bisa ka’ida ba.
A watannin da suka gabata ne dai Bello Bodejo ya kafa kungiyar ‘Zaman Lafiya’ da niyyar samar da kwanciyar hankali tsakanin Fulani da ke fuskantar tashin hankali a sassa daban-daban na Najeriya.
Sai dai gwamnatin kasar ta ce ba a bashi izinin kafa irin wannan kungiya ba don haka ya karya dokar da ta haramta ta’addanci ta shekarar 2022.
An gabatar da shugaban na kungiyar Fulani a gaban Babban Kotun Tarayya na Abuja ranar Juma’a kuma an dage shari’ar da ake yi masa har zuwa ranar 27 ga watan Mayun shekara ta 2024.