Tsaro: Gwamnatin APC Ta Gaza – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, yayi tir da tabarbarewar harkokin tsaro a Kasar,

Inda ya zargi Gwamnatin APC) da Gazawa wajen magance matsalar dake kara ta’azzara.

Da yake kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen Ganin an kare ‘yan kasa da basu ji ba basu Gani ba Daga Masu Garkuwa Da Mutane Atiku Ɗan Takarar Shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a Zaɓen 2023, ya nuna damuwarsa kan yadda Rashin tsaro da ya Addabi al’ummar ƙasar

Rahotannin baya-bayan nan da KBC Hausa ta fitar sun bayyana yadda wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka yi Garkuwa da mutane sama da 200 a jihar Borno a lokacin da suke tara itace a dajin Gamboru Ngala.

Bugu da kari, wasu ‘yan bindiga sun sace ɗaliban firamare da sakandare sama da 200 tare da malamansu a Garin Kuriga dake jihar Kaduna, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin.

A wata sanarwa da ya fitar A Yau Juma’a, Atiku ya soki Gwamnatin dake ƙarƙashin jam’iyyar APC da ƙasa sauke nauyin da ya rataya a wuyan Gwamnati mai cikakken iko wajen Tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan kasa.

Ya koka da cewa, “Matsalar Tabarbarewar tsaro a Najeriya na ƙara ta’azzara a kullum, Tare da munanan abubuwan da suka shafi ‘yan fashi, Garkuwa da mutane, da zubar da jini da ya sanya kasarmu ta kasance cikin yankunan da akafi fama da ta’addanci a Duniya. Ciki har da sace yara ‘yan makaranta sama da 280 a jihar Kaduna, ya nuna Gazawar Gwamnati wajen shawo kan rikicin”.

Atiku ya jaddada cewa a yayin da al’ummar ƙasar ke fama da matsalar Rashin tsaro, Gwamnati na cigaba da yin watsi da marasa ƙarfi tare da yin alkawuran karya Game da kawo sauyi. Yayi kira Ga jami’an tsaro dasu ɗauki kwakkwaran Mataki Domin kubutar da ‘yan kasa da basu ji ba basu Gani ba Daga hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta

Leave a Reply