Tsaro: Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 80 A Yankin Arewa Maso Yamma

Dakarun rundunar operation Sahel Sanity a yankin Arewa maso Yamma sun kashe mahara 80, sun gano bindigogi 7 da shanu 943, in ji Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya bayyana a jiya Asabar.

“Dakarun kwantar da tarzoma na Operation Sahel Sanity, sun gudanar da jerin gwanon ayyuka, kwantan bauna da sauran sintirai a cikin jihohin Sakkwato, Katsina da Zamfara.

“Wadannan aiyyukan sun haifar da kwato wadanda aka sace, dawo da shanun da aka sace, kame wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutane, kame wasu‘ yan bindiga da kuma masu basu bayanai.

“Zuwa yanzu, a cikin dukkan ayyukan da aka gudanar, an kashe yan bindiga guda 80, an kwato shanu 943, an kubutar da tumakai 633;

Kuma An kama wasu ‘yan bindiga da ake zargi guda 33; An gano bindigogi kirar AK47 guda 7, kirar GPMG guda 1 da bindigogi kirar Dane guda 16;

Kuma an kubutar da wadanda aka sace 17 tare da kama wasu masu bada bayanai da aiki da yan bindiga guda 14.

Ya kara da cewa, sansanonin ‘yan bindiga da dama ciki har da sananniyar Dangote Triangle da sansanonin kayan aikinsu, sojojin Operation SAHEL SANITY sun lalata su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply