Sanata mai wakiltar maza?ar Borno ta kudu a majalisar dattawa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, ko ka?an ba’a ?auko hanyar magance matsalar tsaro a kasar nan ba, Wallahi Najeriya ba da gaske take ba wajan samar da tsaro.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja, Sanata Ndume wanda shine shugaban kwamitin kula da sojoji na majalisar Dattijai, yace jami’an tsaron da ake dasu sun yi kadan.
Ya bayyana cewa jimullar duka jami’an tsaron Najeriya, 800,000 ne wanda kuma sun yi kadan su baiwa mutane sama da Miliyan 200 tsaro. Yace duk kasar da ta tsaya a kan haka to ba da gaske take ba.
Yace gaba dayan sojojin Najeriya da a yanzu suke aiki a jihohi 32 na fadin kasarnan su basu kai 160,000 ba, sannan ‘yansanda basu kai, 400,000 ba, yace dan haka akwai bukatar kara yawan jami’an tsaron.