Tsaro: Buhari Ya Kalubalanci ‘Yan Najeriya Su Ba Dakarun Soji Hadin Kai

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa ya yi kira ga ‘yan Najeriya cewa su yi amanna da sojojin ƙasar cewa za su iya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a ƙasar nan.

Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke buɗe Gasar Wasannin Motsa Jikin Sojojin Ruwa Na 12, wato LAGOS 2023.

Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da jajircewa wajen ganin sun samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma sun kawar da ƙalubalen da ya dabaibaye ƙasar nan.

Ya ce dukkan ɓangarori na tsaro za su ci gaba da ɗaukar dukkan matakan da su ka dace wajen tabbatar da kare lafiyar dukkan al’ummar ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana buƙata da muhimmancin haɗin kai da aiki tare tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro da kuma al’ummar ƙasar nan baki ɗaya.

Shugaba Buhari wanda ya sabunta sabuwar cibiyar wasannin Sojojin Ruwa, wadda aka gina kwanan nan, ya jinjina wa Shugaban Sojojin Ruwa CNS Awwal Gambo, bisa gina cibiyar bunƙasa wasannin da ya yi.

“Tsawon shekaru kenan wasanni sun kasance hanyoyin ƙarfafa dangantaka da jituwa tsakanin sojoji tare da cusa ɗa’a a cikin sojoji. Ina mai tabbacin cewa waɗannan wasanni da za a yi za su ba sojojin ruwa damar cimma dukkan ƙudurorin da ke gaban su.”

Buhari ya kuma yi kira da a yi amfanin da cibiyar wasannin ta hanyar da ta dace.

Labarai Makamanta

Leave a Reply