Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta yi kira ga kasashen duniya da su sakar da maran saidawa kasar Makamai da dangoginsa domin taimakata kawar da rashin tsaro dake addabarta yanzu haka
Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, yana mai cewa manyan kasashen na duniya su daina kafa hujjoji ta batutuwa da basu taka kara sun karya ba wajen hanawa kasar cinikin makamai.
A baya bayan nan dai rundunar sojin kasar na cigaba da nuna ƙwanjinta wajen ganin ta fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram dake yankin Arewa maso Gabas da kuma ‘yan Bindiga da ke addabar yankin Arewa maso yammacin kasar.