Tsaro: Arewa Na Tangal-Tangal – Gwamnonin Arewa

IMG 20240315 WA0033

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mai ba Shugaba Tinubu sharawa a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu ya gana da gwamnonin Arewacin Najeriya 19 kan matsalar tsaro dake addabar yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin ganawar wanda ya ta’allaka kan yadda za a dakile matsalar tsaro, gwamnonin sun bukaci sauya fasali a kokarin dakile matsalar tsaro.

Shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya koka kan yadda rashin tsaron ke kara dagulewa a fa?in yankin.

Mai girma Inuwa ya bayyana haka ne a yau Alhamis 14 ga watan Maris bayan ganawa da Nuhu Ribadu da hafsoshin tsaron Najeriya.

Gwamnonin sun bukaci a sauya fasalin yaki da rashin tsaron da ya addabi yankin musamman garkuwa da mutane da neman ku?in fansa.

Gwamna Inuwa ya ce sun yi ganawar ce da Ribadu domin neman sake fasalin dakile rashin tsaron da ke damun yankin. “Makasudin wannan ganawa tsakanin mai ba da shawara a bangaren tsaro da gwamnoni ita ce kawo wani tsari na dakile matsalar tsaro.”

“Wannan ya shafi rashin tsaro wanda ya na da girma sosai musamman sace-sace a yankin Arewa maso Yamma ya kamata a sauya tsarin dakile matsalar.”

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Uba Sani na jihar Kaduna da Umara Zulum na jihar Borno sai Dauda Lawal na jihar Zamfara. Sauran sun hada da Dikko Radda na jihar Katsina da Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da sauransu.

Related posts

Leave a Comment