Tsaro: An Yi Kiran Yin Watsi Da Tsarin Tsohon Shugaban Ghana Rawlings

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa ta gargadi kananan dakarun soji a kan juyawa shugabanninsu baya.

Rundunar ta yi wannan gargadi ne bayan fitar da wani jawabi da aka alakanta da Chidi Chukwuani, shugaban jam’iyyar NDP (National Democratic Party).

A cikin jawabin, Chukwuani ya ce kamata ya yi a kwaikwayi tsarin tsohon shugaban kasar Ghana, John Rawlings, a Najeriya.

John Rawlings, tsohon shugaban kasar Ghana a mulkin soji, ya jagoranci kashe manyan shugabannin sojoji da suka yi kaurin suna wajen cin hanci.

Sai dai, a cikin wani jawabi da kakakin hedikwatar rundunar tsaro, John Enenche, ya fitar ya ce rundunar soji ba za ta dauki kiran da Chukwuani ya yi da wasa ba.

Janar Enenche ya yi wa dakarun rundunar soji tunin cewa sun yi rantsuwa a kan cewa za su kasance ma su biyayya da mika kai ga kasa da kuma shugabn kasa wanda ke zaman babba kwamandan rundunar tsaro ta kasa.

“Ba nufin rundunar tsaro bane ta shiga cacar baki da wani mutum ko wata kungiya ba, amma kalaman da aka yi sun shafi rundunar soji, kuma an yi hakan ne domin a tunzura sojoji,” a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa; “abinda Chidi Chukwuani ya fada daidai ya ke da laifin cin amana da juya baya ga shugabanni da dokokin rundunar soji, wanda bai kamata rundunar soji ta dauki hakan da wasa ba.

“A saboda haka ne, aka bani umarni daga sama a kan na sanar da jama’a tare da yi wa dakarun rundunar soji tunin cewa sun yi rantsuwa a akn cewa za su zama ma su da’a da biyayya ga Najeriya tare da kare kundin tsarin mulkinta.

“Hakan na nufin cewa, a kowanne lokaci, za su kasance ma su mika wuya tare da yin biyayya ga shugaban kasa da kuma sauran mahukunta da masu ruwa da tsaki a gwamnatin Najeriya

“Akwai bukatar dukkan dakarun rundunar soji ta Najeriya su tuna da kundin hukunta laifuka na rundunar tsaro na shekarar 2004, wanda ya yi magana a kan kisan jagoran runduna ko wani shugaba a sashe na 52 da 53.”

Kakakin ya sanar da cewa rundunar soji ba zata bari wata kungiya ta tunzurata wajen yin aiki da gurguwar shawara ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply