Tsaro: An Yi Kira Ga Buhari Ya Jarraba Yin Amfani Da Mayu

Wani mai nazarin Kimiyyan Siyasa, Abdul-Rahoof Bello, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar neman taimako daga wurin mayun Afirka don kawo ƙarshen mastalar tsaro da rashawaa Najeriya.

Tsohon malamin Jami’an da ya bayar da wannan shawarar ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, ya ce ƙaluballen da ke addabar ƙasar za su kai ta su baro, ta tarwatse gaba ɗaya.

Mr Bello ya ce lokaci ya yi da Buhari zai yi amfani da irin wannan tsarin na gargagiya domin kare Najeriya daga hare-haren ƴan ta’addan Boko Haram, cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Ya ce ƙasar ta dade tana amfani da dabara iri guda kuma ba a samun sakamako mai kyau duk da irin addu’o’in da mabiya addinan musulunci da Kirista na kasar ke yi.

Ya yi tambaya a kan dalilin da yasa Shugaban ƙasar har yanzu bai yi garambawul a bangaren tsaro na ƙasar ba duk da kiraye-kirayen da al’umma ke yi na a aikata hakan. Ya tunatar da shugaban kasar cewa Allah (SWT) a cikin Al Kur’ani mai girma ya aike da tsuntsaye daga masu tashi dauke da duwatsu daga gidan wuta su magance wadanda za su kai hari dakin Allah a kan giwaye (Q:105:1-5).

Mai nazarin siyasar ya ce amfani da tsuntsaye da Allah (SWT) ya yi domin magance Mutanen Giwa lamari ne da za a iya kwatanta shi da maita na zamani a ra’ayinsa. Ya koka kan yadda batun rashawa ke ƙara kazanta a kasar kuma ke danƙwafe nasarorin da shugaban kasar ya samu kuma ƴan adawa na iya amfani da wannan wurin yaƙin neman zaɓe.

“Mai ruwa da tsaki a jam’iyyar ta APC ya shawarci shugaban kasar da kada ya karaya ko ya ja da baya wurin dakile muggan da ke kashe-kashe, garkuwa da mutane, rashawa, da ke barazanar ganin bayan Najeriya,” in ji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply