Hukumar tsaftace muhalli ta Jihar Bauchi ta kaddamar da yan’duba gari wadanda zasu rika sa ido a harkokin tsaftace unguwanni don kariya daga daukan chututtuka
Hukumar ta kaddamar da shirin ne a unguwar Doya dake cikin kokowar fadar jihar Bauchin, a karshen mako, tare da shuwagabannin al’ummar yankin da masu ruwa da tsaki a yankunna nasu.
Shugaban hukumar Dr. Kabir Ibrahim ya shaida ma manema labarai a wajen taron cewa, hukumar ta fitar da jaddawalin yadda tsarin aikin yan duba garin tare da kula da hakkin mutane domin samu nasarar aikin da kuma dorewar sa.
Kana yace, “munzo unguwar Doya domin gudanar da tsarin duba gari ya dawo a jihar Bauchi, kuma da sabon tsari, muna kokari muga yaya mutane zasu karbe abun, hakan shi zai bamu daman aiwatardashi sosai saboda mu guji irin abun da yasa tsarin baya ya rushe”
Shugaban ya kara da jadadda aniyar gwamnatin jihar ta waje bada dukkanin abubuwan da ake bukata samun nasarar aikin duba garin.
Mai anguwar Ajiya wanda shine shugaban masu unguwanni a wajen kaddamar da shirin yace “tsarine wanda iyayen mu suka sani kuma anga alfanun sa, sai gashi wan nan hukuma ta dawo dashi, dama su al’umma sun jima suna jiran hakan sakamakon gurbacewan muhalli da yadda ake ko inkula da hidimar tsaftar muhalli”.
Ana shi tsokacin mai ungowar Doya ta tsakiya Malam yusuf mai goro dama abunda muke nema ne ya bace mana amma wan nan gwamnati ta zabi ungowa ta insha Allahu bazamu bada kunya ba zamu tsaya kai da fata muga mun bada tamu guddumuwar wan nan aiki na sa idon yan’duba gari”
A karshe shugaban hukumar ya kara da cewa zasu raba ma’aikatan lungu da sako domin tabbatar da inganci aikin da aka sasu, kuma a cewar sa sannu a hankali zasu karade dukkannin anguwanin cikin jihar Bauchin.