Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar gwamnatinsa kan yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi a fadin kasar. Shugaban kasar a cikin wata sanarwa ta hanun babban hadiminsa ta fuskar watsa labarai, Mallam Garba Shehu a ranar Laraba, ya nuna takaicinsa kan tashin farashin kayan.
Ya yi nuni da cewa bai kamata ace farashin kayan abincin ya tashi a dai dai wannan lokaci dan tattalin arzikin kasar ke kokarin farfadowa ba, sakamakon annobar COVID-19. Shugaban kasar ya ba ‘yan Nigeria tabbacin cewa karin farashin kayan abincin na gajeren lokaci ne kawai, sakamakon shirin da gwamnatinsa ta yi na dai daita lamura.
“Sakamakon samun isasshen ruwan sama, muna sa ran samun damuna mai albarka, wacce za ta samar da amfanin gona mai yawa. “Hakika wannan shekarar mun samu jarabawar da ba a taba yi mana ba tsawon shekaru, ba ma kasarmu kadai ba, fadin duniyar ne gaba daya, tattalin arziki ya durkushe.
“Babbar matsalar da muke fuskanta ba zata wuce ta wasu bata garin ‘yan kasuwa ba, wadanda ke amfani da halin da ake ciki, na kara farashin kayan abinci, ta hanyar boye shi. “Amma domin magance wannan matsalar, gwamnatin Buhari ta amince da sakin kayan abinci da suka hada da tan 30,000 na shinkafa, musamman ga masu kiwon dabbobi.
“Gwamnatin Buhari ta tattauna da manyan masu ruwa da tsaki a harkar abinci musamman na bangaren shinkafa da hatsi, da taimakonsu, za a rage farashin kayan abincin. “Bugu da kari, fannin noma zai mayar da hankali wajen samar da kayayyakin noma musamman taki, da zai taimaka wajen karya farashin abinci, da samar da aikin yi.”