Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Na Wata Shidda

IMG 20240307 WA0056

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?an majalisar wakilan Najeriya sun amince da a zabtare kaso 50 na albashinsu na tsawon watanni shida a wani mataki na nuna tausayawa ga yanayin matsin tattalin arzi?i da yunwa da ?an Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Wannan dai ya biyo bayan amincewa da gyaran ga bu?atar da mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu ya yi na bu?atar ?an majalisar da su sadaukar da kaso 50 na albashin nasu na naira 600,000 da suke kar?a.

Hon Benjamin Kalu ya ce zabtare albashin nasu zai taimaka wa gwamnati wajen sau?a?a wa ?an ?asar rayuwarsu.

Hakan na nufin ?an majalisar wakilan guda 360 za su tara tsabar ku?i har naira miliyan 648 wato fiye da rabin naira biliyan ?aya, idan aka zabtare musu naira miliyan 108 a duk wata

Related posts

Leave a Comment