Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tsadar Rayuwa: Wahalar Da Ake Sha Bata Kai Yadda Ake Surutu Ba – APC

images 2024 03 06T195109.222

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sakataren APC na Ƙasa, Surajudeen Basiru, ya bayyana cewa jadawalin ƙididdigar malejin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci a Najeriya, wanda Hukumar NBS ta fitar kwanan nan, akwai ƙarin gishiri da zuzuta alƙaluma a cikin bayanan.

Basiru ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba, lokacin da ake tattauna da shi a Gidan Talabijin na Channels.

Basiru wanda lauya ne kuma tsohon Sanata, ya yi wannan bayanin daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ta ƙoƙarin kwantar wa matara hankali don kada su fita zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa.

Cikin makon jiya ne dai NBS ta fitar da sabuwar ƙididdigar malejin tsadar abinci, wanda ta ce ya dangwale kashi 40.87, yayin da burkin haƙurin ‘yan Najeriya ya tsinke daidai gangara.

Jadawalin tsadar rayuwa da raɗaɗin hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi wanda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Litinin ɗin nan, sun nuna cewa malejin tsadar kayan abinci ya dangwale zuwa kashi 40.87% bisa 100% a watan Yuni, 2024.

Hakan na nuni da cewa ya ƙaru da kashi 15.62% bisa 100% idan aka kwatanta da gejin sa na watan Yuni 2023, inda a lokacin yake daidai kashi 25.25% bisa 100%.

Haka kuma NBS ta ce malejin game-garin tsadar rayuwa ya haura zuwa kashi 34.19% bisa 100%.

Ƙididdigar ta NBS, wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, tattabar da cewa tsawon watanni biyar kenan aka shafe duk wata kayan abinci da kayan masarufi na fuskantar tashin farashi.

Najeriya ce dai ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Afrika, kuma ƙasa mafiya yawan jama’a a Afrika.

Sai dai kuma ‘yan ƙasar sun afka cikin masifar tsadar rayuwa tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, a ranar 29 ga Mayu, 2023 tun a wurin da aka rantsar da shi.

Tsadar rayuwa ta ƙara tsamari yayin da gwamnatin Najeriya ta yi sagegeduwar sakacin da darajar Naira ta karye a kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

Duk da masifar tsadar rayuwa da ake fama a ƙasar, har yau ana kiki-kaka wajen kasa samun matsaya dangane da batun ƙarin mafi ƙanƙantar albashi, wanda fiye da shekara ɗaya ake ta tsallen-gada a kan sa.

Wannan sabuwar ƙididdiga ta NBS, ta zo yayin da ‘yan Najeriya ke ta kartar ƙasar furucin shirin fitowa su yi wa gwamnati zanga-zanga a ƙarshen watan Yuli.

Idan aka kwatanta malejin tsadar rayuwa na watan Yuni 2023, za a ga ya tsaya ne daidai kashi 22.79. Yanzu kuwa a Yuni 2024, ya dangwale zuwa kashi 33.95, inda cikin shekara ɗaya aka samu ƙarin gwauron tashi da kashi 11.40.

Sai dai sakataren na APC ya ce a yanzu ya tabbatar idan za a sake wata ƙididdigar, to za a ga cewa an samu rangwame.

Ya ce shi da kan sa ya ga ƙididdigar NBS, kuma ya ga cewa tsadar rayuwa da tsadar abinci ya yi sauƙi sosai daga watanni huɗu zuwa yau.

Exit mobile version