Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

?ungiyar ?wadago ta ?asa (NLC) ta bai wa gwamnatin Bola Tinubu wa’adin kwana bakwai ta janye duk tsare-tsaren da ta kira ”masu jefa jama’a cikin wahala” ciki har da ?arin farashin man fetur.

A cikin wata sanarwar bayan taro da ?ungiyar ta fitar, NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023, idan gwamnatin tarayya ta gaza ?aukar matakin da ya kamata.

Sanarwar mai ?auke da sa hannun shugaban ?ungiyar, Joe Ajaero da sakatarenta Emmanuel Ugboaja ta ambato NLC na cewa gwamnatin tarayyar ta nuna halin ko-in-kula kan halin da ‘yan ?asar ke ciki, kuma ta ce gwamnatin ta kaddamar da ya?i ne a kan ma’aikata da talakawa.

?ungiyar ?wadagon ta ce tun daga lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, ”hankalin ‘yan Najeriya bai kwanta ba”.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce cire tallafin man fetur ?in ya zama wajibi a halin da ?asar take ciki, matu?ar tana son samun ku?a?en gudanar da muhimman ayyuka.

Exit mobile version