Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin Bola Tinubu wa’adin kwana bakwai ta janye duk tsare-tsaren da ta kira ”masu jefa jama’a cikin wahala” ciki har da ƙarin farashin man fetur.
A cikin wata sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar, NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023, idan gwamnatin tarayya ta gaza ɗaukar matakin da ya kamata.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero da sakatarenta Emmanuel Ugboaja ta ambato NLC na cewa gwamnatin tarayyar ta nuna halin ko-in-kula kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki, kuma ta ce gwamnatin ta kaddamar da yaƙi ne a kan ma’aikata da talakawa.
Ƙungiyar ƙwadagon ta ce tun daga lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, ”hankalin ‘yan Najeriya bai kwanta ba”.
Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce cire tallafin man fetur ɗin ya zama wajibi a halin da ƙasar take ciki, matuƙar tana son samun kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka.