Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-Zangar Gama Gari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya, ta baiwa gwamnatin kasar wa’adin kwanaki goma sha hudu domin cimma matsayar da za ta rage radadin cire tallafin mai da ‘yan Najeriya suka shiga ko kuma fuskantar zanga-zangar ma’aikata.

A halin yanzu Najeriya na fama da matsalar tsadar rayuwa. Farashin sufuri da farashin abinci na ci gaba da hauhawa tun a watan Mayu bayan da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin man fetur.

Shugaban kungiyar, Mista Nuhu Toro ya shaida wa BBC a ranar Talata cewa kungiyar ba ta ji dadin tafiyar hawainiyar da ake yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin ba.

“Wani bangare na fahimtar da muka yi da gwamnati shi ne cewa a cikin makonni 8 ya kamata a samar da ingantattun matakan tallafi wadanda za a iya tabbatar da su kuma za a aiwatar da su cikin lokacin da aka amince.”

“An kafa wasu ƙananan kwamitoci da za su yi aiki don warware matsalolin. Amma makonni hudu bayan hakan, ƙananan kwamitocin uku ne kawai suka nuna cewa sun yi wani abin a zo a gani. Wasu kwamitocin ba su fara aiki ba.”

“Mun bayar da shawarar biyan mafi karancin albashi na N200,000 (kimanin $300) amma kamar yadda muke magana, kwamitin da ke aiki kan mafi karancin albashi bai zauna ba.”

Kungiyar ta bayar da wa’adin ranar 19 ga watan Agusta domin kammala tattaunawa ko kuma ta dauki wani mataki na kare ma’aikata da talakawa daga halin kuncin tattalin arziki.

Baya ga fara rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin mulki, TUC ta ce ya kamata gwamnatin tarayya da jihohi su rage yawan almubazzaranci da kuma rage yawan kudin da ake kashewa.

An dai nuna bacin rai game da karin farashin man fetur a fadin ƙasar inda a baya-bayan nan kungiyoyin kwadago suka yi barazanar janyewa daga tattaunawa da gwamnati.

Kungiyoyin sun zargi gwamnati da cire tallafin man fetur ba tare da fara aiwatar da matakan dakile illar da za ta yi wa ‘yan Najeriya ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply