Tsadar Rayuwa: Ku Kara Hakuri Sauki Na Nan Tafe – Tinubu Ga ‘Yan Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roki ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa sauƙi na nan tafe.

Ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya ɗauki alhakin matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnatinsa.

Tinubu ya kara da cewa ba zai yi ƙorafi ba, amma yana maraba da duk sukar da ake yi masa tunda shi ne ya nemi zama shugaban Najeriya.

Me za ku ce game da wannan ban haƙuri da shugaban ƙasar ya yi wa al’ummar ƙasa?

Ya zuwa yanzu wane mataki ne cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka kuke ganin an ɗauki hanyar kawo sauƙin rayuwa ga al’umma?

Labarai Makamanta

Leave a Reply