Gamayyar ?ungiyoyin arewacin Najeriya ta CNG, ta bai wa shugaban ?asar Ahmed Bola Tinubu wa’adin mako guda da ya hanzarta tare da yin nazari game da halin da al’ummar ?asar ke ciki, tare da ?aukar matakan gaggawa da za su kawo wa ?an Najeriyar sau?in rayuwa.
?ungiyar dai ta ce dole ce ta sa daukar wannan mataki sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa musaman tashin farashin kayayyaki a ?aukacin fa?in ?asar.
Gamayar ?ungiyoyin arewacin ta Najeriya ta ce, lamarin ?angin da ake fama da shi a ?asar ya fi ?amari a yankin arewacin ?asar, saboda yanayin da al’ummar yankin ke ciki.
Kwamared Jamilu Aliyu Chiranci shi ne shugaban ?ungiyar ta CNG, ya shaida wa BBC cewar Najeriya na tunkarar wani mataki mai hadari, saboda wahalhalun tattalin arziki, da hauhawar farashi, da talauci da ya yi wa ?an ?asar katutu.
“Duk abinda shugaban ?asa zai yi, akwai bu?atar ya tsaya ya mayar da hankali kan ceto ?asar nan, wanda ina da ya?inin cewar bazai so a ce a lokacin sa Najeriya ta shiga yanayin da ?an ?asar za su yi mata turjiya ba”
Sannan ya ce ’mutam miliyan 133 a Najeriya na fama da talauci, sannan mutane miliyan 20 ba su da aikin yi ko ma a ce ba su da isasshen aiki”, In ji Kwamrated Chiranci.
”Mutane na cikin ?imuwa da damuwa sakamakon matsalar masu garkuwa da mutane, sannan ga hauhawar farashi kaya da ta kai kashi 34.19, farashin kayan masarufi irin abinci ya karu da kashi 40.66 sababnin yadda ya same shi” In ji Kwamradet Jamilu Aliyu Chiranci.
Ya kuma yi kira ga shugaba Ahmed Bola Tinubu da ya magance tushen dukkan matsalolin da suka haifar da hauhawar farashin mai, da ?arin kudin wutar lantarki, da na kayan abinci, ga faduwar darajar Naira, da tsadar tafiyar da gwamnati da amincewa da wasu tsare tsare da ke kuntatawa talaka.
Haka kuma kwamaret Chirancin ya yi watsi da shirin ?ara farashin mai don samar da sabon mafi karancin albashi na kasa, tare da kira ga shugaba Tinubu da ya sallami tawagarsa ta tattalin arziki ya kuma dauki sabbin hanyoyin da za su magance matsalar tattalin arzikin da ke addabar kasar.
Sannan ya yi Allah wadai da ?arin kudin ruwa da gwamnatin ta yi, wanda ta ce ba komai zai ba sai kara jefa tattalin arziki cikin matsala, da rage damar sama ayyukan yi.
shugaban gammayar ?ungiyoyin arewacin na Najeriyar Kwamaret Jamilu Aliyu Chirancin ya ce ba a ta?a samun gwamantin da aka sami koma baya ba a Najeriya, kamar mulkin Bola Ahmed Tinubu ba, wanda maimakon a sami ci gaba sai ma koma baya a ake ta samu, saboda manufofin da gwamantin ta ke futo da su babu wanda zai ce tana jin ?asan talakan ?asar.