Tsadar Rayuwa: Buhari Ya Buƙaci Matasa Su Koma Gona

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen farfado da fannin noma don samar da wadataccen abinci da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasar ya ce mayar da hankali a fannin noma zai taimaka wajen rashin dogaron kasar da fannin danyen mai, musamman wajen kasafin kudi.

Wasu daga cikin tsare tsaren shugaban kasar na farfado da tattalin arziki sun hada da rufe iyakokin kasa domin bunkasa noman shinkafa, da dakile masu shigo da abinci kasar.

“Ina kara jaddada cewa daga yanzu babban bankin Nigeria ba zai kara bayar da canji ga masu shigo da abinci ko taki a kasar ba. “Ba zamu biya ko kwabo na kudaden ajiyar waje ga masu shigo da kayan abinci ko taki ba.
Maimakon hakan, zamu bunkasa manomanmu na cikin gida,” cewar Buhari.

Shugaban kasar ya kuma karfafa guiwar matasa akan su koma noma, kasancewar farashin danyen mai na ci gaba da durkushewar a kasuwar duniya.

Taken gwamnatina ya kasance, “Dole mu ci abunda muka noma, kuma dole mu noma abunda zamu ci.”

“Muna da matasa masu jini a jika da ke da burin aiki, to noma shi ne mafita ga kowa,” a cewarsa.

Shugaban kasar ya sha suka daga shekarar 2018 a lokacin da ya kira matasan kasar a matsayin “cima zaune”. Mun ruwaito muku cewa a ranar 18 ga watan Afrelu 2018, a taron kungiyar kasashe masu takama da kasuwanci a Westminster, ya ce matasan Nijeriya na jira gwamnati ta yi masu komai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply