Tsadar Rayuwa: Albashin 100,000 Ya Yi Wa Ma’aikaci Karanci – Majalisa

IMG 20240307 WA0056

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara tsananta, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, majalisar wakilai ta yi kira da a biya ma’aikatan Najeriya albashi mai kyau.

Majalisar ta kuma umarci kwamitocin kwadago da samar da ayyuka, kuɗi da tsare-tsare da su tsara hanyoyin biyan albashin ma’aikatan Najeriya a farashin da ya yi daidai da yanayin tattalin arziƙin da ake ciki.

Da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya sa talakawan Najeriya cikin wahala. Ya yi nuni da cewa biyan buƙatun yau da kullum da suka haɗa da abinci, ruwa, gidaje, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tufafi, da sauransu na neman gagarar ƴan Najeriya.

A cewarsa: “Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya yi mummunan tasiri a kan tsadar rayuwa, inda farashin abinci, wurin kwana, ilimi, da sufuri ya yi tashin gwauron zabi.” Duba da yanayin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke ciki, majalisar ta yi nuni da cewa babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa a Najeriya da albashi ƙasa da N100,000 a kowane wata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply