Tsadar Rayuwa: Addu’o’in Da Manzon Allah Ke Yi – Sheikh Sani Khalifa

A wannan gaba da muke ciki na tsananin rayuwa saboda tsadar abinci da talauci, babu abinda zai fitar da mu sai addu’a, maimakon yawan zagi da zargi ya kamata mu koyi abinda manzon Allah saw yake yi idan ya rasa abinci a gidansa. Imamul Tabarani ya ruwaici hadisi cewa : wata rana manzon Allah saw zai yiwa bako liyafa sai ya aika wajen matayensa da a nemo abinci, da aka je sai ba’a samu abinci a wajen dukkan matansa ba, da aka dawo aka fada masa cewa babu abinci a gidansa sai ya karanta wadannan addu’oin :

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ وَرَحْمَتِكَ، فَإِنَّهُ لا يَمْلِكُهَا إِلا أَنْتَ،

[[Allahuma inni as aluka min fadlika wa rahmatika, fa innahu la yamlikuha illa anta.]]

Ance yana gama karanta wadannan addu’oin sai aka kawo mishi hadaya na gasahiyar akuya, sai yace : wannan daga falalan Allah ne, yanzu muna jiran rahamarsa.

Saboda haka mu rike wadannan addu’oin mu yawaita karanta shi musamman a cikin wannan lokaci da muke ciki na tsadar rayuwa insha Allahu Allah zai yaye muna, bayan na mu rinka yawaita karanta wannan ayar :

رَبِّ إِنِّي لِمَا أَنْزَلْتَ إِلَيَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ

Ita ce addu’ar da annabi Musa A.s ya karanta a lokacin da ya shiga kuncin rayuwa da talauci Allah ya yaye masa.

Su kuma masu mulki su sani cewa babu wani aiki akansu mai muhimmancin fiye da samarwa talakawa da abinci da kayan more rayuwa.

Zawiyyar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria, Mataimakin shugaban kungiyar Fityanul Islam ta kasa
11/09/2020

Labarai Makamanta

Leave a Reply