Madugun Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokradiyya maimakon zanga-zanga.
Kwankwaso Ya bayyana hakan ne A cikin wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu a ranar Jumma’a 26 ga Yuli, 2024 Ya shiga cikin rashin jin dadi da kan kiraye-kirayen zanga-zangar da matasan ke Shirin gudanarwa a duk fa’din Kasar.
Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa Amma t hanyar karfin zabe.