Karamin Ministan Fetur, Timiprey Sylva, ya bayyana cewa sannu a hankali jama’a za su saba da karin kuɗin mai, har ya zame masu jiki.
Sylva ya bayyana haka a lokacin da ya fito daga ganawar sirri tare da Shugaba Muhammadu Buhari, a Fadar Shugaban Kasa.
Ya ce ya gana da Buhari ne inda ya yi masa bayanin matsalar da kasar nan ke ciki, dangane da rashin samun kudaden shiga wadatattu.
Ya ce a yanzu kudaden shigar da Najeriya ke samu daga fetur da harajin cikin gida (FIRS), ya ragu matuka da kashi 60 cikin 100.
Ya ce yanzu ba a samun kuɗi da fetur saboda karyewar darajar farashin ɗanyen mai a duniya.
Sannan kuma ba a samun kuɗaɗen shiga daga harajin cikin gida tun bayan da cutar korona ta barke a kasar nan.
“Wadannan dalilai sun sa ruyuwa ta yi taanani ga ‘yan Najeriya.
“Duk da haka ya zama tilas gwamnati ta daina biyan kudaden tallafin man fetur. Domin idan ta ci gaba da biya, a wannan yanayi da ake ciki, to za a wayi gari ko albashin ma’aikata ba za a iya biya ba.
“Daina biyan tallafi shi ya kawo tsadar fetur, domin gwamnatin tarayya ta daina kwasar kudi ta na biyan dillalan mai da sunan tallafi. Shi ya sa kasuwa ce a yanzu ke yanka wa litar fetur farashi.
“Sannu a hankali jama’a za saba da karin kudin fetur. Zai zama jiki, kamar yadda aka saba da karin gas da kananzir, wadanda sun ma fi amfani ga ƴan Najeriya fiye da fetur.” Inji Sylva.
Rahoton Premium Times